05/08/2025
Nafisa Abdullah Aminu, 'yar shekara 17, ɗaliba 'yar Jihar Yobe da ke Arewacin Nijeriya, ta fafata da ɗalibai 20,000 daga ƙasasher 69, inda ta zo ta ɗaya a duniya a gasar iya Turancin Ingilishi, wato English language skills 2025 TeenEagle Global Finals da aka gudanar a birnin London.