Engnr Shafi'u Garba Arg

Engnr Shafi'u Garba Arg Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Engnr Shafi'u Garba Arg, Convenience Store, Masallachi malam musa fakkai, Argungu.

YAU ZAN BAKU GORON JUMMA'A MAI MATUƘAR ZAFI DA ZURFI...Wannan ba rubutun da zaka karanta da sauri ka wuce ba ne. Ka nats...
01/05/2026

YAU ZAN BAKU GORON JUMMA'A MAI MATUƘAR ZAFI DA ZURFI...

Wannan ba rubutun da zaka karanta da sauri ka wuce ba ne.

Ka natsu ka kalli rayuwa ta waɗannan ɓangarorin guda 5 waɗanda muke yawan yi wa kanmu ƙarya a kansu:

1.
Kullum cewa kake "zan fara gobe", "zan nemi sana'a idan na samu jari", "zan gyara ibadata idan na ɗan yi gaba". Baka lura cewa shekarunka satarsu ake yi a gaban idonka ba? Jiya kana da 20, yau ga ka a kusan 30, gobe ƙarfinka ya ƙare. Lokaci baya jiran ka shirya, kuma mutuwa bata duba cikar burinka kafin ta ɗauke ka.

2.
Akwai miliyoyin mutane a ƙarƙashin ƙasa waɗanda s**a mutu da manyan tsare-tsare masu matuƙar kyau a ransu, amma tsoron fara aiki ya hana su tabbatar da su har ranarsu ta zo. Kada ka bari tsoron faɗuwa ko tsoron abin da mutane za su ce ya sa ka koma ga Mahaliccinka da tarin burika ba tare da ka cika ko ɗaya ba. Ka Gwada a Koda zaka faɗi sau dubu, gara ka faɗi wajen neman nasara, a kan ka zauna kana kallon masu yi.

5.
Ka ɗaga hannu kana roƙon Allah Ya buɗa maka wannan ranar Jumma'a, amma da an idar da sallah zaka koma majalisa ka yi zaune kana jiran mu'ujiza. Wannan ba tawakalli ba ne, wasa ne da hankali, Addu'a babu fafutuka, mafarki ne kawai. Fafutuka babu addu'a, wahalar banza ce. Haɗa su biyun.

Dan'uwa, idan har numfashinka yana shiga yana fita a wannan lokacin, to Allah Yana baka wata sabuwar dama ce domin ka gyara lissafin rayuwarka..

Allah ya amshi ibadunmu na wannan ranar mai girma, ya yaye mana ƙuncin zuciya, kuma ya buɗa mana ƙofofin alheri ta inda ba mu yi tsammani ba.

Barka da Jumma'a.

*🔥 Me yasa sallah take hana alfasha ?* 002.*Ya ku bayin Allah!*  Sallah ba kawai motsa jiki bace – *ganawa ne tsakaninka...
26/02/2026

*🔥 Me yasa sallah take hana alfasha ?* 002.

*Ya ku bayin Allah!* Sallah ba kawai motsa jiki bace – *ganawa ne tsakaninka da Allah.* Idan kayi sallah da zuciya, zata gyara zuciyarka, kuma zata hana ka aikata fasadi da mummunan hali.

*Allah (SWT) ya ce:*

﴿إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنْهَىٰ عَنِ ٱلْفَحْشَآءِ وَٱلْمُنكَرِ﴾

*_Lallai sallah tana hana alfasha da mummunan aiki."_* [Al-Ankabut: 45]

*✨ Ta yaya sallah ke hana fasadi ?*

- *Ta tsarkake zuciya...* kana tuna Allah sau 5 a rana, wannan yana ratsa ranka.
- *Ta horar da zuciya:* kana koyon da'a, hakuri, da tsoron Allah.
- *Ta hana kusanci da zunubi:* ka sani cewa kana cikin tsarki kuma zaka koma sallah.

*Annabi (SAW) ya ce:*
> Me kuke tunani da wani wanda kogi yake gudana a bakin ƙofar gidansa, yana wanka a cikinsa sau biyar a rana ? Shin zai rage masa datti ?
> S**a ce: E mana.
> Ya ce: Haka sallah take wanke zunuban bawa.” – [Bukhari & Muslim]

*⚠️ Idan har kana sallah amma kana cikin fasadi....*

- Sai kayi tambaya... *“Wace irin sallah nake yi ?”*
- Domin sallah ta gaskiya tana canza hali.
- Ka gyara zuciyarka kafin ka tsayar da jiki.
-

> *Ka gyara sallah, zata gyara rayuwarka.”*

> *Idan sallah bata hana ka daga zunubi, to baka yi sallah ba, ka dai yi motsin jiki ne kawai.”*

*Ya Allah!* Ka sanya sallar mu ta zamo kariya daga fasadi, ka ba mu ɗanɗanon ibada, ka karɓi sallolinmu da zuciya ɗaya.

*الله تعالى أعلم*

29/01/2026

I accepted 1 fan badge from Zauren Sheikh Aliyu Rasheed Makarfi.

*MASU MULKI KUJI TSORAN ALLAH 😭* 001.*KU RIKE AMANA 🔥*Ya ku masu mulki! Mulki ba girmamawa ba ne kawai – jarabawa ce dag...
28/01/2026

*MASU MULKI KUJI TSORAN ALLAH 😭* 001.

*KU RIKE AMANA 🔥*

Ya ku masu mulki! Mulki ba girmamawa ba ne kawai – jarabawa ce daga Allah. Kujerar da kuke kai, ba naku ba ce, amana ce a wuyanku😭

Allah Madaukaki ya ce:

> ﴿إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِ﴾

*Allah yana umartar ku da ku mayar da amana ga masu ita, kuma idan kun yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi da adalci.*

Ya ku masu mulki! Talakan da kuke rainawa a yau, watakila shi ne hujja ko laifinku gobe a gaban Allah.

Allah ya ce:

> ﴿وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّٰلِمُونَ﴾

*Kada ku yi zaton Allah bai san abin da azzalumai suke aikatawa ba.*

Mulki ba ya hana mutuwa😭
Kujera ba ta hana shiga kabari 🔥

Iko ba ya hana tambaya a Lahira 📚

Manzon Allah (SAW) ya ce:

> Duk wanda Allah ya ba shi alhakin jagorantar jama’a, ya yaudare su – Allah zai haramta masa Aljanna.” 😭

Ya ku masu mulki! Hawaye na marayu, kuka na mata, yunwar talakawa – duk suna hawa sama. Kada ku ce “ba mu sani ba.”

Allah ya ce:

> ﴿وَقِفُوهُمۡ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ﴾

*Ku tsayar da su, lallai za a tambaye su.* 😭

Umar bn Khattab (RA) ya ce:

> Da jakin Iraqi ya yi tuntuɓe, ina tsoron Allah ya tambaye ni me ya sa ban gyara masa hanya ba.” 😭

Ya ku jama’a! Kada ku ɗauki zalunci ku kira shi siyasa. Zalunci zalunci ne, ko daga waye ya fito.

*Wallahi*
Mulkin da aka gina da adalci – yana dawwama.
Mulkin da aka gina da zalunci – yana rushewa, ko da ya ɗauki lokaci.

الله تعالى أعلم

26/01/2026
Sheikh Bashir‎ akwai baiwar ilimi,‎Ilimi  ya  sallami  jahilci.‎‎Ga nan haƙuri kuma ga tsafta,‎Sannan kuma ba ya ɓatanci...
18/01/2026

Sheikh Bashir‎ akwai baiwar ilimi,
‎Ilimi ya sallami jahilci.

‎Ga nan haƙuri kuma ga tsafta,
‎Sannan kuma ba ya ɓatanci.

‎Ya san kimiya ya gane,
‎Ya san sharri na yáhudanci.

A fagen nan ba mu da tamkatai,
Ya gano dukkan makirci.

Ya san sharri na mutanen can,
Ya gane dabarar kâfurci.

Ya binciki ârna ya san su,
Ya tona asirin ârnanci.

‎A fagen nazari shi ne tuta,
‎Ba hutu b***e yin barci.

‎Ya san boko ga addini,
‎Bai bokanci sai bokonci.

‎Ya gane Bukhari har Muslim,
‎Masani ne gun addinanci.

‎Ba ya girman kai ko ta sule,
‎A ziyara kam ya san naci.

‎Makusanta sun shaida cewa,
‎Wayayye ne ba ƙauyanci.

Burinmu a ce ya fito Gwamna,
Da irin su ake jagoranci.

‎Bai son gaba ba ya gaba,
‎Jagora ne gun sasanci.

‎Yara manya sun san malam,
‎Malam shi ya wuce inganci.

‎Ga imani ga inganci,
‎Kuma sannan ba ya lalaci.

‎Kowa ai ya gano malam,
‎Malam shi ba ya shashanci.

‎Malami kamar wasu malumma,
‎Amma shi nashi da bambanci.

‎Lafiya ka ƙara mar Allah,
‎Har ya samu dukkannin ƴanci.

✍️ Ahmad

*IYAYEN  MU – 001* *Su ne dalilin samuwarka. Kada ka manta da su, ko bayan sun riga mu gidan gaskiya.😭**Ya ku bayin Alla...
10/01/2026

*IYAYEN MU – 001*

*Su ne dalilin samuwarka. Kada ka manta da su, ko bayan sun riga mu gidan gaskiya.😭*

*Ya ku bayin Allah!* Iyayenmu su ne tushen rayuwarmu. Su ne s**a ɗauki nauyinmu tun muna cikin ciki, s**a wahala saboda mu, s**a yi kuka saboda mu, s**a yi addu’a domin mu… *to me muka mayar musu da shi ?*

Allah (SWT) Yana cewa:

﴿وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُواْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًا﴾

*_"Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa wani sai Shi kaɗai, kuma a kyautatawa iyaye."_* [Al-Isra: 23]

*Abubuwan da ya kamata mu kula da su......*

*1. Yin biyayya da girmamawa*
> Kada ka daga murya a gabansu, kada ka ƙi bin umarni su, kada ka yi musu magana mai zafi.

*2. Yi musu magana mai taushi da ƙauna*
> Kamar yadda s**a kula da kai da tausayi, kai ma ka nuna musu kulawa da taushi.

*3. Addu’a domin su – musamman idan sun riga mu gidan gaskiya*
> *“Ya Allah ka gafarta wa iyayena, ka saka musu da alheri, ka sa kabarinsu ya kasance lambun Aljanna.”*

*4. Yin sadaka mai gudana a madadinsu*
> Gina rijiya, bayar da Al-Qur’ani, koyar da ilimi, da sauran ayyukan alheri da suke ci gaba da kawo musu lada.

*5. Ka cigaba da ɗaukaka sunansu da kyautata musu a cikin mutane.*
> Kada ka manta da su cikin addu’a, zance, da aikace-aikace.

> *Idan iyayenka suna raye, ka rike su da hannunka biyu – domin ran da za ka neme su ka rasa yana iya zuwa nan da ƙanƙanin lokaci😭.”*

> *Idan sun rasu, kada ka bar girmamawa da biyayya ya mutu tare da su😭.”*

*Ya Allah!* Ka gafarta wa iyayenmu. Ka saka musu da alheri. Ka sa su huta a kabarinsu fiye da yadda s**a hutad da mu a bayyane da boye.

*الله تعالى أعلم*

Address

Masallachi Malam Musa Fakkai
Argungu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Engnr Shafi'u Garba Arg posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share