Labaren hausa

Labaren hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Labaren hausa, Newsstand, Abuja.

Wannan wani dan haqiqa ne bangaren Tijjaniyya mai suna Baye. Ya ce komai daidai ne. Maƙala Cross da shan giya.Ku me kuka...
31/10/2023

Wannan wani dan haqiqa ne bangaren Tijjaniyya mai suna Baye. Ya ce komai daidai ne. Maƙala Cross da shan giya.

Ku me kuka ce?

YANZU-YANZU: Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Da Atiku Ya Ƙalubalanci Nasarar TinubuA ranar Alhamis ɗin nan ne k...
26/10/2023

YANZU-YANZU: Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Da Atiku Ya Ƙalubalanci Nasarar Tinubu

A ranar Alhamis ɗin nan ne kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa, wanda ya kawo ƙarshen ƙalubalen shari’a da manyan abokan hamayyarsa biyu s**a shigar, inda s**a ce nasarar da ya samu ba halastacciya ba ce.

Hukuncin dai ya bai wa Tinubu mai kimanin shekaru 71 da haifuwa nasarar cigaba da shugabancin ƙasar da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afirka, wadda ke fama da hauhawar farashin kayan masarufi, da ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje da taɓarɓarewar Naira, da rashin tsaro da kuma satar ɗanyen mai.

Hukuncin da wasu Alkalan kotun kolin guda bakwai s**a yanke, wanda shine na ƙarshe, ya biyo bayan wani salon da aka gani a zaɓukan da s**a gabata na shugaban ƙasar da aka ƙalubalanta a gaban kotu. Babu wani yunƙurin soke sak**akon ta hanyar kotuna da ya yi nasara.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour ne s**a zo na biyu da na uku a zaɓen watan Fabrairu, amma s**a ƙi amincewa da sak**akon, s**a kuma yi kira da a soke nasarar da Tinubu ya samu.

Shugabannin ‘yan adawa biyu sun ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba wanda ta amince da nasarar Tinubu.

Alkalin kotun ƙolin John Okoro ya ce “Babu cancantar su Atiku da Obi su ɗaukaka ƙarar, don haka yace sun yi watsi da ita.”

Wadannan da kuke gani k**a su akai da laifin Garkuwa da karamin yaroAna zargin su da laifin Garkuwa Da wannan yaron ne m...
26/10/2023

Wadannan da kuke gani k**a su akai da laifin Garkuwa da karamin yaro

Ana zargin su da laifin Garkuwa Da wannan yaron ne mai suna Al Mustapha a karamar hukumar Mubi Jahar Adamawa.

Yanzu haka anyi nasarar k**asu bayan Yaron ya kwana Daya a hannunasu.

KUNCIN RAYUWA: Wadanda S**a Ba Ni Shawara Na Baro Saudiyya Na Dawo Nijeriya, Àĺĺàh Ýà Ìśà Tsakanina Da Ku, Cewar Alh Ami...
26/10/2023

KUNCIN RAYUWA: Wadanda S**a Ba Ni Shawara Na Baro Saudiyya Na Dawo Nijeriya, Àĺĺàh Ýà Ìśà Tsakanina Da Ku, Cewar Alh Aminu Ay II

HOTUNA: Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Alhaji Abba Elmustapah kenan lokacin da ya halarci saukar Alqur'a...
26/10/2023

HOTUNA: Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Alhaji Abba Elmustapah kenan lokacin da ya halarci saukar Alqur'ani na ƴar cikin sa mai suna A'isha.

A'isha ta haddace Alqur'ani mai girma ne, tana da shekara 12 a duniya

Wane fata za kuyi mata?

© LABAREN HAUSA

DA ƊUMI ƊUMINSA: Babban Bankin ƙasa CBN ya ayyana ƙudurinsa a yau Alhamis na cewa zai sauya fasalin wasu takardun kuɗi n...
26/10/2023

DA ƊUMI ƊUMINSA: Babban Bankin ƙasa CBN ya ayyana ƙudurinsa a yau Alhamis na cewa zai sauya fasalin wasu takardun kuɗi na ₦200 ₦500 da kuma ₦1000.

Naira dubu 50,000 aka biya Sadakin ko wane Aure, guda dubu 1800 da aka daura a shirin Auren zawarawa a jihar Kano, idan ...
24/10/2023

Naira dubu 50,000 aka biya Sadakin ko wane Aure, guda dubu 1800 da aka daura a shirin Auren zawarawa a jihar Kano, idan ka lissafa dubu 50 sau 1800 zai baka nera miliyan 90 daidai, kuma Gwamnan jihar Kano ya biya duka; Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Tura ɗalibai karatu ƙasashen waje ƙarya ne da coge, kuma wallahi wasu jami'oin namu na Gida sunfi na ƙasashen wajen naga...
24/10/2023

Tura ɗalibai karatu ƙasashen waje ƙarya ne da coge, kuma wallahi wasu jami'oin namu na Gida sunfi na ƙasashen wajen nagarta.

Kalaman tsohon gwamnan Kano kuma shugaban riƙon jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya furta a matsayin martani bayan tura Ɗalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf tayi a baya bayan nan, domin su yi karatun Digiri na biyu.

Me zaku cé?

DA ƊUMINSA: Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya! Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rar...
24/10/2023

DA ƊUMINSA: Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya!

Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya sanya gasar wata sabuwar waka da yayi akan shirin gwamnatin tarayya na ƙidaya da za'a gudanar a farkon shekarar 2024, inda ya bayyana muhimmancin ƙidaya ga yan ƙasa Nigeria.

Aisha Humaira wacce abokiyar aikin Rarara ce, tayi bayanin yadda ƙidayar za ta taimaka a sha'anin tsaro, tare da bayani akan yadda gasar za ta kasance da kuma irin kyaututtukan da za'a bayar ga wadanda s**a shiga gasar, da s**a hada da Mota, Babur da kuma kuɗi.

Sai dai kuma gasar bata samu karɓuwa ga ma'abota shafukan sada zumunta musamman TikTok ba, inda wasu jaruman dandalin ke ganin Rarara bai shiga lamarin kira ga gwamnati akan matsalar tsaro da ake shan fama a Arewacin Nigeria ba, saboda haka a yanzu shima ba zasu karɓi bukatarsa ba.

Kano State Sponsored Students in Sharda University.
23/10/2023

Kano State Sponsored Students in Sharda University.

Happy birthday Al'ameen shu'aibu money! You've got a magic that will wow the worldInjibaban sa Adam A zango
23/10/2023

Happy birthday Al'ameen shu'aibu money! You've got a magic that will wow the world

Injibaban sa Adam A zango

Kotun ta kololuwa ta karbi korafin dan takarar PDP ne a yau Litinin, abin da wasu ke ganin wata nasara ce ga Atiku Abuba...
23/10/2023

Kotun ta kololuwa ta karbi korafin dan takarar PDP ne a yau Litinin, abin da wasu ke ganin wata nasara ce ga Atiku Abubakar a kan wannan batu.

Nan gaba ne kotun za ta bayyana lokacin yanke hukunci bayan ta yi nazarinta.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaren hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category